NI MA DABBA NE

NI MA DABBA NE 



Ina jiyoshi cikin yanayi na “khushu’i” yana kuka ta amsa-kuwwar da ke jikin katon masallacinsa da akaiwa lakabi da “Masjidul Islah”. Yana ta karaji kamar ransa zai fita saboda al’umma ta lalace. Da alamun wa’azin ya shiga jikin daruruwan almajiran da suke zaune a gabansa wadanda mafi yawansu talakawa ne irinsa kafin ya hadu da yan siyasa. Kowa ya yi shiru a nutse kamar tsuntsu ne akansa, sai yar kabbarar da ke tashi nan da can idan wa’azin ya tsuma wani saurayin daga gefe - “Allahu Akbar!” 

Ya fara da cewa dole ne idan ana son a gyara Najeriya to sai an rufe gidajen giya da na karuwai domin wadannan zunuban su ne suka janyo mana ci baya. Wannan maganar ba yau na fara jin ta ba. Shekara hudu haka da ta gabata kafin Mallam Yusufa ya tafi karatun digirinsa a birnin Texas shi ma haka ya dinga cewa a laccar “pre-khutba” din da yake yi duk Juma’a. Daga baya ne da ya zo hutu na ji yana fadawa abokinsa yadda kasar Amurika ta samu ci gaban da ya kayatar da shi, amma bai fada masa ko a can din ma akwai gidajen giya da na karuwai ba duk da na san an ce kafirai Allah ya tsine musu tun da ba sa banbance halal da haram komai ma yi suke. Ina son yin tambayar nan, to amma dai na taba jin wani limami yana cewa yawan tambayoyi shi ne ya halakar da mutanen baya don haka kowa ya kame bakinsa ya yi shiru; ni ma na yi. 

Ni ba wannan ne ya dameni ba, domin sha’aninku ne na mutane. Mu dabbobi muna da yadda muke bautawa Allah kuma ba zaka taba jin karen Jamus ya yaki karen Ghana ba. Wannan wani sha’aninku ne na mutane masu rigima da kuke sakomu a cikinku. Mu bama ma gane ina ne gabas bare kuma yamma. Na sha kokarin wayar da kan wasu karnuka da muke yawon tsintar kasusuwa a bakin bola cewa hadin kai shi ne kadai zai cecemu daga illar da mutane suka yi mana, amma yan uwana sun ki ji. Duk biyayyar da muke musu su a ganinsu bamu da zuciya ne. Shi yasa suke kwatanta yan uwansu masu rashin zuciya da cewa suna abu kamar karnuka. Wannan magana tana bata min rai don haka na gwammace da zama da Bila Mai-dabba akan wani gida da na taba zama da basu da abin yi sai saka wani yaro a gidan ya dinga cukwuikuyata. Da rannan ya cijeni na rama suka koreni. Da na sake komawa basu hakuri suka ce bani da zuciya. Daga nan na koma bola tsince-tsince har Mai-dabba ya tsince ni muke fita farauta. Watakila ma ni ne sanadin shiga aljannarsa tun da ran nan ai na ji wani malami a Islamiyyar da na wuce ya ce wata karuwa ta shayar da kare kuma ta shiga aljanna. To duk wiwin ko da Mai-dabba yake sha ai za a yafe masa musamman ni har mushe yake kawo min na yini ina ci. 

Bara dai na fada muku ko wani malami na fara magana akansa, ba batun boye-boye. Ranar wanka ba a boyen cibi in ji masu yin wankan. Sheikh Inusa Mai Littafi ne ya ci gaba da cewa wai daga laifukan da ya sa Najeriya ta kasa ci gaba har da ajiye karnuka wanda sabon Allah ne. Kai sai ka dauka ba shi na ji wata rana a tafsiri yana cewa wasu matasan Kogo tare da karensu suka gudu suka je bakin inda suka buya suna bacci ba. Kuma shi da kansa ya ce yan aljanna ne har da karen nasu. To ta yaya masu ajiyemu za su shiga aljanna idan sabo suke? To amma ya ce wai ya zo a littafin hadisi cewa gidan da aka ajiye kare mala’ikun rahama basa shiga. Ya fadi marawaicin hadisin da ba zan iya tunashi ba, amma dai wata rana da na shiga kasuwa tsince-tsince na ji wani dan Qur’aniyyun yana cewa wai da alamun wanda ya fadi hadisin mage yake kiwo shi yasa ya ce ajiyemu debe lada yake. Ba sai na gaya muku gabar da take tsakaninmu da wannan karamar halittar mara godiyar Allah sai bacci da son jiki ba. Amma wai har an zabeta an ce mu rikemu zunubi ne! Saboda Allah da mu da ita wa ya fi amfani? Na san ba tsoron Allah kuke ba balle ku fadi gaskiya don mafi yawanku ku ne masu tafiya shafin Muneerat Abdussalam ku kalli bidiyonta. Sai ka ga “views” 300,000 amma masu “comments” duk tsine mata suke. Ku tsine mata ku dawo sake kallonta. 

Kuma ma fa na san abin da ya sa Sheikh Inusa ya tsanemu. Abokina Bitrus, wanda shi ma kare ne irina, shi ne ya jaza mana. Wata rana da daddare bayan kowa ya shiga gida na hango Sheikh Inusa ya zo shiga dakin karatunsa da wata yarinya yar unguwar da nake. Yarinyar ta lullube fuskarta amma na ganeta saboda kowa ya san duk unguwarmu ba wanda ya kaita shafe-shafe. Lokacin da na santa baka ce sosai kamar kafarta, amma yanzu fuskarta ta koma kamar ta baturiya sai dai kafar har yanzu baka ce. Ni ma ta haka na ganeta. Ni dai na san Sheikh Inusa ba dan Qadiriyya ba ne amma bayan minti biyar da shigarsu na ji sun fara zikirin amfasu. Ni da yake na ga shigarsu ban ce komai ba. Amma Bitrus na zuwa ya fara haushi, zatonsa ko wani barawon agogon ne ya sake dawowa masallaci don ya yi abin da ya saba. Nan take ya katse musu zikiri. Ina ji Sheikh na cewa ki yi sauri ki fita kada wani ya fito amma sai na sa an kwashe karnukan nan. Ina ji daga nan ya fara cewa wai mu ne matsalar Najeriya. 

Ranar da yake wannan jawabin dan majalisar tarayya na karamar hukumarmu ya zo masallacin kuma ya yi alkawarin bayar da gudunmawarsa wajen sake ginin masallacin da kuma fadada gidan mallam. An ce dan majalisar ma daga gayyatar EFCC ya tawo gida don ya huta kuma ya hakurkurtar da magoya baya. Ai kam ya samu addu’o’in nasara a wannan masallaci. Ina ji ina gani aka ce taimakonmu ta hanyar bamu gurin zama shi ne matsalar Najeriya amma kuma shi dan majalisar da ya zo aka yi masa addu’ar sake komawa mulki. Haka mutane suke yi mana. Su dinga barin jaki suna dukan taiki don sun san mu ba magana muke yi ba. Kuma ko da aka ce a ji tausayin dabbobi to ai ni ma dabba ne.

Aliyu Ɗahiru Aliyu 

@Aliyussufiy a Twitter. 

Comments

Popular posts from this blog

LGBT+ Agitations and Arewa Society

Climate change and security implications for Northern Nigeria.

Shame, Shamelessness and the price to be paid.