Munafunci a Arewa.



 Ban taba ganin al’ummar da kwarewarta a munafunci yake bani mamaki ba kamar ta Hausawa. Da Ibn Salul zai zo nan, da kansa zai gane shi karamin munafuki ne. A iya bincikena, al’ummar nan ne suka fi kowa tafiya nemo duk wani abu mai kama da batsa a shafukan Internet, amma a nan ne kowa zai nuna maka shi fa na Allah ne da ko mace ce ba mayafi sai ya fara tsine mata albarka. 

Da dalilin da ya sa shafukan jaridu irin su BBC suke koya harkokin kwanciya da iyali. Ba wai da ka suke yi ba. Dubawa suka yi ta hanyar abin da ake kira “analytics” suka gano masu karatunsu suna son batsa, don haka suka kawo musu abin da suke so. Dazu nake ganin wani na cewa me yasa ko CNN basa irin wannan amma sai BBC Hausa? Amsar ita ce ita BBC ta san su waye masu karatunta don haka tana kawo musu abin da suka fi karantawa (clicks) ko dannawa “comment” da “likes”. Domin ba abin da aka fi so a al’ummar nan bayan musun addini don a boye aibuka sai harkar fim din Hausa da hirar batsa. 

Duk shafin da ake “searching” da aka fi zuwa, kamar Google ko YouTube, ka danna farkon wani rubutu da zai bada aiki da Hausa to sai ka ga aikin da Hausawa suke a lokacin da suke zaton Allah ba ya ganinsu. Wadanda suka fi tsinewa yan iskan Facebook don su nunawa na waje na Allah ne su, su suka fi shiga shafinsu. Shi yasa ko a YouTube da “content creators” suke neman a tsaya kallonsu don su samu kudin shiga, za ka ga yan matan nan da suke batsa sun fi kowa samun “views”. Amma masu abu mai muhimmanci basa samun komai. 

A lokacin da ka tafi kallon batsa, ba ka tunanin Allah yana ganinka? Baka jin tsoron kowa sai ni da na tona kana yawon neman batsa sai ka fara yi min wa’azin yada barna saboda ka boye abin da kake yi don a dauka kai waliyyi ne? Ni za ka yiwa karya da munafunci? Amma Allah yana ganinka kuma “Google Analytics” na biye da kai. Idan yau na karbi wayarka ko da ka goge duk “browser history” dinka, baka san ina da “ethical hacking tools” da zan dawo da duk abin da ka taba shiga ba? 

Ko da ban kawo “screenshot” din abin da kuka fi shiga kuna tambaya ba, da farko dai Allah yana ganinku. Abu na biyu kuma ba yadawata ce take janyowa kana iskancewa ba - dama can kai dan iskan ne. Tona maka asiri kawai na yi. Kuma shigarka da yawan tambayoyinku ita za ta bawa masu kirkirar wani bidiyon su sake yin na batsa ba wai tonawar da na yi ba. Don haka BBC ba za su dena koya kwanciyar iyali ba, haka masu batsa a TikTok da YouTube ba za su dena ba, saboda irinku suna nan suna zaginsu amma suna labewa suna kallonsu suna jin dadi. Kai ka ma yarda da Allah kuwa da za ka dinga yin wannan wasan? A gaban duniya ka nuna kai mumini ne amma a gabansa ka dinga iskanci?

By Aliyu Dahiru Aliyu. 

@Aliyussufiy on Twitter. 

Comments

Popular posts from this blog

LGBT+ Agitations and Arewa Society

Climate change and security implications for Northern Nigeria.

Shame, Shamelessness and the price to be paid.